Crime·

Ƴan bindiga sun yi awon gaba da shugaban ƙaramar hukumar Bungudu

Ƴan bindiga sun yi awon gaba da shugaban ƙaramar hukumar Bungudu
Source:rfi_fr

A Najeriya ,rahotanni daga jihar Zamfara, na bayyana cewa ƴan bindiga sun yi awon gaba da shugaban ƙaramar hukumar Bungudu Nura Umar Bungudu.

Ƴan bindiga sun yi awon gaba da shugaban ƙaramar hukumar Bungudu A Najeriya ,rahotanni daga jihar Zamfara, na bayyana cewa ƴan bindiga sun yi awon gaba da shugaban ƙaramar hukumar Bungudu Nura Umar Bungudu. Wallafawa ranar: Rahotanni daga yankin Bungudu ,na bayyana cewa maharan sun kai hari garin ne a daren Alhamis kuma suka nufi kai tsaye zuwa gidan shugaban ƙaramar hukumar da ke yankin Zango, kasa da kilomita 20 daga babban birnin jihar, Gusau. Wani mazaunin garin,da ya bukaci a sakaya sunansa ya ce 'ƴan bindigar sun fi karfin jami'an tsaro da ke tsaron gidan, inda suka kashe 'ƴansanda biyu da 'yan banga biyu kafin su fice da shugaban ƙaramar hukumar Bungudu Nura Umar Bungudu da iyalansa. A kokarinsu na mayar da martani,jami’an tsaro sun ceto wasu daga cikin yara da ƴan bindiga suka sace. "Sun sace shugaban tare da matarsa da 'ya'yansa,duk da kokarin jami’an tsaro,ƴan bindigar sun fice da shugaban ƙaramar hukumar. "Jami'an tsaro sun yi iya ƙoƙarinsu, amma lokacin da sojoji suka isa wurin, 'yan bindigar sun fice daga yankin ga baki ɗaya. Wani mazauni kauyen ya ɗora alhakin ƙaruwar irin waɗannan hare-haren musaman ta yada ƴan bindigar ke samun kudade na fansa da kuma amfani da manyan makamai,baya ga samun ƙarin bayanai daga masu tallafa musu.

This is a summary. Read the full article at the original source.

Read full article at rfi_fr